News
Buhari zai ziyarci Zamfara gobe Alhamis
Daga kabiru basiru fulatan
Gwamna Bello Matawalle na Zamfara ya baiyana cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar a gobe Alhamis.
Gwamnan ya baiyana hakan ne a yayin wani taron gaggawa da ya yi da ɗaukacin masu rike da muƙaman siyasa a zauren majalisar zartsawar jihar a ranar Talata da daddare.
A cewar Matawalle, makasudin ziyarar shugaban kasar shine jajantawa kan hare-haren ta’addancin da a ka kai ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum, inda aka kashe mutane da dama.
Matawalle ya ce: “An shirya komai don ganin an tarbi shugaban cikin nasara.
“Ina so in sanar da daukacin al’ummar Jihar Zamfara cewa Babban Kwamandan Tarayyar Najeriya zai zo Zamfara a ranar Alhamis, musamman domin ziyarar jajantawa kan hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum na jihar. .”
Gwamnan ya bukaci ɗaukacin al’ummar jihar da su kasance masu bin doka da oda yayin ziyarar shugaban ƙasar.