News
Buhari ya soke zuwa Zamfara
Daga kabiru basiru fulatan
Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya soke ziyarar da zai kai Jihar Zamfara a yau Alhamis.
Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle me ya baiyana hakan.
A jiya Laraba ne dai Gwamnan ya baiyana cewa Buhari zai kai ziyarar a yayin wani taron gaggawa da ya yi da ɗaukacin masu rike da muƙaman siyasa a zauren majalisar zartsawar jihar a ranar Talata da daddare.
A cewar Matawalle, makasudin ziyarar shugaban kasar shine jajantawa kan hare-haren ta’addancin da a ka kai ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum, inda aka kashe mutane da dama.
Amma kuma a wata sanarwa da ta fita a yau, Matawalle ya ce Buhari ya soke ziyarar ne sakamakon rashin kyawun yanayi.
Sai dai kuma ya ce shugaban ƙasar zai sake sanya wani lokacin domin ya kai ziyarar ta jaje da ta’aziyya a jihar a makon gobe.