News
Mutum shida sun ji rauni a hatsarin da helikwafta ya yi a Bauchi
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Mutum shida ne suka ji mummunan rauni a hatsarin da wani helikwafta mallakin rundunar ƴan sandan Najeriya ya yi a Bauchi a jiya Laraba.
Gidanrediyongwamnatin tarayya ya ruwaito Hukumar Bincike Haɗurra ta ƙasar, AIB tana tabbatar da labarain.
Saidaia sanarwar da hukumar AIB ta fitar ɗin ta ce babu wanda ya mutu a hatsarin.H
ukumarta ce Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya NAMA ce ta sanar da ita faruwar lamarin kuma tuni an fara bincike.
Hukumartanemi duk wanda lamarin ya faru a kan idonsa ko ya naɗi wani bayani na faruwarsa da ya kai mata don taimaka wa wajen binciken da ake yi.
AIBta kuma buƙci jama’a da ƴan jarida da su tsare sirrin waɗanda hatsarin ya rutsa da su ta hanyar dakatar da yaɗa jita-jita kan abin da ya haddasa hatsarin har sai an fitar da bayani a hukumance.