Connect with us

News

Da yuwar a kara ciwo sabon bashi — Buhari

Published

on

FB IMG 16432628411004175
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce, da yiwuwar Najeriya ta ci gaba da ciyo bashi, domin ci gaba da biyan tallafin man fetur.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke magana ta cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels TV da safiyar Laraba.

A cewrsa: “Ko ma dai yaya ne dole ne Najeriya ta ji a jikinta. Ko dai mu ɗanɗana kuɗarmu a matsayinmu na ‘yan ƙasa…ko kuma gwamnati ta ci gaba da ciyo bashi, wanda ba zai yi wa gwamnatin tarayya da jihohi kyau ba a tattalin arziki.

Advertisement

“Kun san irin yawan kuɗin da za a adana idan aka soke tallafin sannan kuma a saka su cikin wani fannin na ƙasa. Idan ba a yi hakan ba a yanzu – na yarda ba abu ne mai sauƙi ba a yanzu – to fa dole ne mu ɗanɗana kuɗarmu.”

A shekarar da ta gabata Majalisar Dattawa ta amince wa gwamnatin Buhari ta ciyo bashi iri-iri, ciki har da na dala biliyan 6.1, sai kuma na dala biliyan 16 da wani na yuro biliyan ɗaya a watannin Yuli da Nuwamba kowannensu.

Akwai yiwuwar gwamnati ta kashe naira tiriliyan biyu da rabi cikin shekara ɗaya da rabi da gwamnatin ta ce za ta ci gaba da biyan tallafin. A cewar BBC.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *