Connect with us

News

Yara goma (10) da aka yi wa kisan gilla a Najeriya

Published

on

Spread the love

Daga kabiru basiru fulatan

 

 

Advertisement

 

 

Kisan yara yana daga cikin kashe-kashe masu muni a ban-ƙasa, saboda yara a kan kalle su a matsayin farin-ciki rayuwa, waɗanda ba su da wani laifi da suka yi wa kowa. To amma sai ga shi rashin imanin wasu gardawan har ya wuce kan kashe manya, sun koma kisan yara ƙanana, waɗanda ba su yi wa kowa komai ba. Da ma dai tun a ‘yan shekaru kamar goma da shuɗe ne dai rayukan al’umma suka zama arha a Najeriya, musamman ma a Arewacin ƙasar.

Advertisement

An kashe ɗaruruwan yara saboda zalunci. Wannan ne ya sa kafar BBC ta tattara wani rahoto ya yara goma (10) da aka hallaka a Najeriya, duk da cewa akwai yaran da aka kashe da yawa, to amma ba zai yiwu a iya kawo su duka ba. Ga rahoton BBC.

“A shekarun baya-bayan nan za a iya cewa an samu ƙaruwar cin zarafin yara ta hanyar muzguna musu da wulaƙanta rayuwarsu da ma kashe su a Najeriya.

Duk da cewa babu wasu alƙaluma a hukumance da ke nuna yadda ƙaruwar ke hauhawa, amma abubuwan da suke faruwa a kewayenmu waɗanda kafafen yaɗa labarai ke ruwaito kawai sun isa a kafa hujja cewa yara na fuskantar munanan ƙalubale a wannan ƙarnin.

Advertisement

Kama daga yi musu fyaɗe da azabtar da su da yin safarar su da sacewa don neman kuɗin fansa da kuma sace su don sayar wa iyayen da ba sa haihuwa zuwa kashe su a wuraren da yaƙi da rikici ya yi ƙamari da kuma mayar da su ƴan gudun hijira ƙarfi da yaji.

Mafi munin abin da suke fuskanta kuma shi ne kisa, musamman ta hanyar yi musu kisan gilla.

A wasu yanayin kuma ko da sun tsira da ransu a irin harin da aka kai musu, to yaran kan dauwama cikin firgici sakamakon mummunan halin da aka saka su a ciki.

Advertisement

Waɗannan shekarun baya-bayan da ma waɗanda muke ciki yanzu, an samu yawaitar fyaɗe ga yara ƙanana, wasu ya yi sanadin kashe su, wasu kuma ya saka su a yanayi maras kyau.

Sannan babban abin tashin hankalin ma shi ne yadda makarantu, wuraren da ake ganin tudun mun tsira ne ga yara, a yanzu sun fara zama wuraren da iyaye ke zama cikin fargaba idan ƴaƴansu sun tafi.

A Najeriya an ga yadda aka dinga kai hare-hare makarantu ana sace yara tare da yin garkuwa da su, ciki kuwa har da masu ƙananan shekaru.

Advertisement

A wasu lokutan kuma, wasu ɗaliban ne ke cin zarafin wasu ta hanyar zalintarsu, kamar yadda ya faru a wata makaranta a Maiduguri kwanan nan.

Mafi muni da sanya ɓacin rai kuma shi ne wanda malaman ne ma ke zama silar mutuwar wasu yaran ko yi musu wani mugun abu, duk da amincewar da iyaye suka yi na damƙa musu amanar ƴaƴansu, kamar dai yadda ake zargin wani malamin makaranta a Kano da sacewa tare da kashe ɗalibarsa Hanifa Abubakar mai shekara biyar.

Wannan maƙala ta yi waiwaye kan labarai na wasu yara 10 da suka taɓa fuskantar “kisan gilla” a sassan Najeriya, waɗanda kuma suka ta da hankalin ƴan ƙasar.

Advertisement

Wasu alƙaluma da asusun yara na Majalisar Ɗinkin Duniya Unicef ya fitar sun nuna cewa shekarar 2021 an kai hari sau 25 a kan makarantu, an kashe yara 16 sannan an sace yara 1,440.

Mun zaɓi labarai na yara 10 ne saboda ba za mu iya kawo labaran dukkan yaran da suka taɓa fuskantar irin wannan lamari ba.

Haidar ɗan shekara huɗu – Na’ibawa Kano

Advertisement

A shekarar 2014 a unguwar Na’ibawa da ke birnin Kano a arewa maso yammacin Najeriya, an sace wani yaro ɗan shekara biyar mai suna Haidar.

An sace shi ne a watan Maris a gaban makarantar Islamiyyarsu bayan an tashi. Yana tsaye yana jiran budurwar da ke tafiya da shi Islamiyya, sai wani ya kama hannunsa ya tafi da shi.

Haidar ya shafe kwana biyu a hannun waɗanda suka sace shi, kuma sun faɗi kuɗin fansa har an saka musu a asusun bankin da suka bayar.

Advertisement

Bayan biyan makuɗan kudin fansar, sai suka faɗi wajen da za a ɗauke shi amma ko da aka je sai gawarsa aka samu sun saka a cikin buhu sun ajiye a wajen.

Kisan Haidar ya jefa iyayensa da ɗaukacin al’ummar birnin Kano da ma na Najeriya cikin ɗimuwa.

Daga baya jami’an tsaro sun yi aikinsu wajen binciko waɗanda ake zargi da aikata laifin, wadanda kuma mutum uku ne mazauna unguwar su Haidar, wato dai maƙwabtansu ne suka aikata wa ƙaramin yaron wannan ta’asa.

Advertisement

An gurfanar da su a gaban kotu kuma an yi ta tafka shari’a inda a ƙarshe tabbatattun majiyoyi suka shaida wa BBC cewa an yanke musu hukuncin kisa. Sai dai kawai za a iya cewa tabon da suka bari a zuciyar iyaye da ƴan uwan Haidar ba zai taɓa warkewa gaba ɗaya ba.

Kashe yarinya da jefa ta a rijiya bayan yi mata fyaɗe a – Rigasa Kaduna

A shekarar 2018 ne aka nemi wata yarinya mai shekara takwas aka rasa sama ko ƙasa – a unguwar Rigasa da ke Jihar Kaduna.

Advertisement

Daga baya da aka tsananta bincike, sai aka gano gawarta a wani gida a unguwar da ke maƙwabtaka da gidan iyayenta.

An gano gawar tata ne a cikin wata rijiya a gidan sannan wuyanta a karye. Binciken da hukumomi suka yi bayan samun gawar ya nuna sai da aka yi mata fyaɗe sannan aka karya wuyan nata, kuma aka jefa gawar a rijiya.

A lokacin, BBC ta yi hira da iyayenta da suka tabbatar da ana bincike a kan lamarin, kuma wanda ake zargin maƙwabcinsu ne.

Advertisement

Zuwa yanzu, babu wani labari kan inda aka kwana da batun binciken ko sakamakonsa.

Aisha Sani – Kano

A watan Yunin 2019, an sace wata yarinya mai suna Aisha Sani a Unguwar Tudunwada da ke cikin birnin Kano.

Advertisement

Wata mata ce aka yi zargin ta sace Aisha a hanyarta ta komawa gida bayan tashinsu daga makarantar Islamiyya, kuma mako biyu bayan haka ne aka tsinci gawar Aisha.

Aisha na tafiya gida ne tare da ƴan uwanta yayin da wata mata, wadda ta rufe jikinta ruf har fuska, ta ɗauke ta. Ba a tuntuɓi iyayen Aisha ba har tsawon kwana uku bayan sace ta.

Sun nemi a ba su naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa kuma suka buƙaci mahaifiyar yarinyar ce za ta kai kuɗin.

Advertisement

Daga baya dai da aka tsananta bincike, an tsinci gawar Aisha an daddatsa ta aka jefar da gawar.

Babu tabbas kan me ya faru tun bayan hakan ta fannin binciken makasanta da batun shari’arsu.

‘Yan sanda na bincike kan bidiyon da matasa suka zane ‘ƴan mataYadda matashi ‘ya sace tare da kashe’ dan yayarsa a Kano

Advertisement

Yaro mai shekara takwas – Karkasara Kano

A watan Yulin 2019 din dai kuma rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta kammala bincike domin gurfanar da wasu matasa da take zargin cewa su ne suka sace wani yaro dan shekara biyar, wanda ya rasu a hannunsu, ciki har da ƙanin mahaifiyar yaron.

‘Yan sanda sun kama matasan uku ne a Unguwar Karkasara.

Advertisement

An sace yaron ne da hadin bakin wanda ke raka shi makaranta, inda suka nemi a basu naira miliyan 50, a cewar rundunar ƴan sandan jihar.

Bayanai sun ce wadanda suka sace shi sun ba shi ƙwayoyi sannan suka ɗaure masa baki, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa, sannan suka binne shi a wani kango.

Ƴan sandan sun ce mutuwar yaran ce ta sa suka rage kudin da suka nema zuwa 100,000.

Advertisement

Dubunsu ta cika ne bayan da suka fito karbar kudin da suka nema, inda jami’an ƴan sanda suka yi musu kwantan-bauna, sannan suka kama su.

‘Yan sanda sun kuma tono gawar yaran, wadda suka ce babu abin da ya same ta.

Abin takaici da rashin imani shi ne barayin, wadanda shekarunsu suka kama daga 19 zuwa kasa, na da alaka da iyayen yaran ne.

Advertisement

Babu tabbas a yanzu kan halin da ake ciki game da shari’ar mutanen.

‘Uwa ta kashe ƴaƴanta biyu’ a Kano

A watan Oktoban 2020 ne kuma aka shiga wani hali na ruɗu a birnin Kano, bayan da aka yi zargin wata uwa da kashe ƴaƴanta har biyu a Unguwar Sagagi.

Advertisement

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar yaran, Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da ‘yar uwarsa Zahra’u Ibrahim mai shekara uku.

Yusuf da kanwarsa Zahra’u tare da mahaifinsu

Yaran da ake zargin mahaifiyar tasu ta kashe su ne Yusuf Ibrahim mai shekara biyar da ‘yar uwarsa Zahra’u Ibrahim mai shekara uku kuma sun gamu da ajalin nasu ne ranar Asabar.

Advertisement

Dangin mijin matar sun yi zargin cewa matar ta aikata hakan ne sakamakon sabanin da ta samu da mijinta saboda ya yi mata kishiya a watannin baya.

Sai dai su kuma iyayen matar sun ce ƴar tasu ta daɗe tana rashin lafiyar da ke da nasaba da iskokai.

Jami’an tsaro dai sun ce uwar sassara ƴaƴan ta yi da adda da taɓarya.

Advertisement

Sannan ita matar ta shaida wa ƴan sanda cewa yaran ne suka ɗauki wuka suna neman halaka ta, daga nan kuma ta shiga dukansu da taɓarya da kuma sassare su da adda.

Daga baya dai an kai ta asibitin masu taɓin hankali don duba lafiyarta da kyau.

Lamarin ya ɗaure wa mutane da dama kai saboda ba a saba ganin uwa ta kashe ƴaƴanta da hannunta ba.

Advertisement

Fyaɗe a Kaduna – Yarinya ƴar shekara shida

A watan Yunin 2020 kuma an tsinci wata gawarta da aka jefar a wani masallaci a Kaduna bayan yi mata fyaɗe.

Lamarin ya faru ne a ranar wata Juma’a a wani masallaci da ke unguwar Kurmin Mashi, a karamar hukumar Kaduna Ta Kudu.

Advertisement

Wani Mazaunin unguwar ne ya fara ganin gawar yarinyar yashe a cikin masallacin inda nan take mutane suka taru suna nuna takaicinsu da kuma mamaki.

An nemi yarinyar ƴar shekara shida an rasa ne daga fita waje wasa, inda daga baya aka ga gawar a masallacin. Lamarin da ya tayar da hankalin jama’a da dama.

A lokacin da abin ya faru ƴan sanda da hukumomin jihar Kaduna sun tabbatar da ƙaddamar da bincike. Sai dai zuwa yanzu ba a san inda aka kwana kan maganar ba.

Advertisement

Sylvester Oromoni, ɗalibi mai shekara 12 – Lagos

Ana zargin ɗaliban da suka kashe Sylvester sun yi hakan ne don ya ƙi shiga ƙungiyarsu ta asiri

Kisan Sylvester Oromoni, wani ɗalibi mai shekara 12 a wata makarantar kwana a jihar Lagos ya ɗaga hankali sosai a Najeriya.

Advertisement

A watan Disamban 2021 ne aka wayi gari da labarin mutuwar ɗalibin, wanda ake zargin wasu ɗalibai ƴan uwansa ne ƴan ƙungiyar asiri suka kashe

Bayanai sun ce sun yi hakan ne don ya ƙi shiga cikinsu.

Mutanen sun ci zarafinsa sosai ta yadda har sai da aka kwantar da shi a asibiti ranar Juma’a, sai kuma ya rasu a ranar Talata, kwana hudu bayan nan.

Advertisement

Binciken da aka gudanar a asibiti ya nuna cewa yaron ya samu raunuka sosai ta can cikin jikinsa sakamaon mugun dukan da aka yi masa.

Mohammed Kabiru mai shekara shida – Kaduna

Muhammad Kabiru mai shekara shida ya haɗu da ajalinsa a hannun wasu mutane da suka sace shi suka kuma nemi kuɗin fansa a hannun iyayensa a watan Mayun 2021 a jihar Kaduna da ke Najeriya.

Advertisement

Maƙwabtan mahaifan yaron a Unguwar Badarawa ne ake zargi da aikata hakan, inda suka sace shi tare da guduwa da shi jihar Kano.

Da farko sun nemi a ba su naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa, amma daga baya aka daidata a kan naira miliyan ɗaya, kuma bayan sun karɓi mahaifin yaron Kabiru Magayaki, sai kuma suka kashe shi, kamar yadda rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar.

Bayan da aka tsananta bincike ne sai aka kama mutum huɗu da zarginsu da hannu a sacewa da kashe yaron.

Advertisement

A lokacin dai ƴan sanda sun tabbatar da gurfanar da su a gaban ƙuliya, sai dai zuwa yanzu babu wani bayani kan halin da shari’ar tasu ke ciki.

Kisan Hanifa ya ɗaga hankalin al’umma

Kisan Hanifa shi ne na baya-bayan nan da ya ɗagawa mutane hankali sosai a shafukan sada zumunta da ma tsakanin waɗanda ba sa amfani da shafukan.

Advertisement

An sace ta tun ranar 4 ga Disamban 2021 a hanyarta ta komawa gida daga islamiyya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu mutane ne suka ɗauke ta a A Daidaita Sahu suka tafi da ita. An yi ta nema da cigiya amma sai bayan kwana 46 aka samu jin ɗuriyarta.

Ko a lokacin ma ba a samu Hanifa a raye ba, don tuni wadanda suka sace tan sun kashe ta ta hanyar ba ta maganin ɓera da yi mata gunduwa-gunduwa tare da saka ta a cikin buhu suka binne ta a makarantar da ta zam can take karatun boko.

Advertisement

Wanda ake zargi da aikata wannan ta’asa ba wani ba da ya wuce malaminta a makarantar bokon, kuma mamallakin makarantar, wanda shi da bakinsa ya shaida wa ƴan sanda batun. Ya kuma raka su inda ya binne ta har aka tono gawar tata aka sake yi mata sutura.

Tuni ƴan sanda sun miƙa lamari ga kotu, inda za a fara sauraron ƙarar ranar 2 ga Fabrairun 2022.

Za a iya cewa labarin Hanifa ya karaɗe ciki da ma wajen Najeriya, kuma mutane sun zuba ido don ganin irin hukuncin da hukumomi za su yanke wa mutumin da sauran abokansa biyu da suka taya shi wannan aika-aika.

Advertisement

‘Abubuwan da zan riƙa tunawa da su game da ƴata Hanifa’Kisan Hanifa ya fusata ƴan Najeriya

Husnah, shekara tara – Zariya

Ana tsaka da tashin hankalin kisan Hanifa ne sai kuma labarin kashe wata yarinya Husnah mai shekara takwas ya fara yaɗuwa.

Advertisement

BBC ta tuntuɓi mahaifin Husnah, Alhaji Wa’alamu Uban Dawaki ya kuma tabbatar da cewa an sace ƴarsa ne tun a ƙarshen shekarar da ta gabata, kuma ta shafe kwana 41 a hannun waɗanda suka sace ta.

Ana zargin maƙabcin su Husnah da sace ta

“Sun nemi kuɗin fansa kuma mun aika musu har naira miliyan 3,549,000, amma bayan aikawar ba su sako ta ba.

Advertisement

“Daga baya jami’an tsaro suka duƙufa aikinsu suka kuma gano wanda ake zargi da hakan, wanda maƙwabcina ne ga gida ga gida.

“Ya amsa cewa ya sace Husnah ne a ƙofar gida da misalin ƙarfe biyu na rana ta je sayen katin waya,” in ji Alhaji Wa’alamu.

Mahaifin yarinyar ya ci gaba da cewa wanda ake zargin ya tabbatar wa ƴan sanda cewa tuni shi da abokan harƙallarsa sun kashe Husnah har ma sun binne ta a wani waje.

Advertisement

“Amma har yanzu ya ƙi faɗar inda ma suka binne tan don mu tono mu ga gawarta mu sake suturta ta. Sannan ya ƙi bayyana mana sauran abokan hulɗar tasa.”

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *