Connect with us

News

An hana zirga-zirga a yayin ziyarar shugaban Najeriya a Gusau

Published

on

Spread the love

Daga muhammad muhammad zahraddin

A ranar Alhamis ɗin nan ne Shugaba Muhammadu Buhari zai sauka a Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a wata ziyarar wuni guda da zai kai.

Tun a jajiberin ziyarar gwamnatin Zamfara ta bayar da sanarwar dakatar da zirga-zirgar ababen hawa ta tsawon sa’a uku a yayin ziyarar ta shugaban ƙasa.

Advertisement

Gwamnatin jihar dai ta ce ahugaban na Najeriya zai je Zamfara ne domin jajanta wa al’ummar jihar game da miyagun hare-haren ‘yan fashin daji na baya-bayan nan musamman a ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

Kwamishinan Yaɗa labarai na jihar Zamfara, Malam Ibrahim Magaji Dosara, ya shaida wa BBC cewa tuni suka kammala shirye-shiryen tarbar shugaban kasar.

Ya ce baya ga ta’aziyya da jajen da Shugaba Buhari zai yi wa al’ummar ta Zamfara, zai kuma kara wa sojoji Najeriya da ke jihar kwarin gwiwa a kan irin samame da sauran ayyukan da suke yi wajen fatattakar ‘yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar da ma sauran jihohi.

Advertisement

Kwamishinan Yaɗa labaran ya ce daya daga cikin manufar ziyarar shugaban kasar a Zamfara ita ce domin ya sanyaya zukatan al’ummar ta Zamfara tare da nuna musu cewa yana tare da su.

Malam Ibrahim Dosara ya ce,” Ba jajen Anka da Bukkuyum kadai Shugaba Buhari zai yi ba, zai yi jaje ne ga dukkan iyalan wadanda suka rasa wani nasu a hare-haren ‘yan bindigar a jihar Zamfara”.

A cewarsa a yayin ziyarar shugaban kasar zai gana da jami’an tsaron da ke aiki a jihar da malamai da sarakunan gargajiya da kuma iyalan wadanda suka rasa ransu a yayin hare-haren.

Advertisement

Tuni dai gwamnatin jihar ta bukaci al’ummarta da su kiyaye da dukkan wasu dokoki a yayin ziyarar shugaban kasar.

Al’ummar jihar da ma wasu a sauran jihohi sun jima suna tsokaci a kan rashin zuwan shugaban Najeriya Zamfara don jajantawa al’ummar jihar a kan irin masifar da suke gani ta hare-haren ‘yan fashin daji.

Jihar Zamfara dai na daya daga cikin jihohin Najeriya musamman a yammacin kasar da ke fama da hare-haren ‘yan fashin daji da satar mutane abin da ala tilas mazauna yankuna da dama na jihar suka bar muhallansu don tsira da ransu.

Advertisement

Kusan kananan hukumomin jihar na fuskantar wadannan hare-hare, inda hatta noma ma a wasu yankunan aka daina saboda yadda fashin dajin ke kai wa manoma hari su kashe su a cikin gonakinsu.

To ko wanne tasiri ziyarar shugaba Buharin zata yi wajen tabbatar da tsaro a jihar ta Zamfara? wannan shi ne abin da al’ummar yankin ke jira su gani.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *