News
Gwamnatin Kano ta fara aiwatar da dokar hana sha da sayar da shisha
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kai simame shagunan da ake sayar da shisha a kan titin Bompai da ke jihar Kano a jiya Laraba, inda ta samu nasarar kama dillalan shishar, domin tabbatar da dokar hana sha da siyar da ita a jihar.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa wannan shine karo na farko da gwamnati ta fara aiwatar da dokar a faɗin jihar, tun bayan da majalisar dokoki ta sanyawa ƙudurin dokar hannu.
Sashi na 13(7) na dokar sisha, wacce a ka sanyawa hannu a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2021, ya ce sha da ta’ammali da shisha haramun ne a Jihar Kano.
Tuni dai hukumar ta fara kama masu sayar da shisha a jihar, inda su ma su ka ce duk da an hana, har yanzu a na kawo musu ita da ga Dubai da China.
Sun yi ƙorafin cewa an fara aiwatar da dokar me ba tare da an basu wa’adin su dena ba.
Sun kuma ƙara da cewa ya kamata a ce an wayar musu da kai da kuma sanarwa mai tsawo kafin a zo a fara kai musu farmaki a wajajen sana’ar su.
Sun ce su sun zaci dokar ta tsaya ne a wajen masu guraren shan shishar ba wai dillalin ta ba.
Da ya ke ganawa da manema labarai, Shugaban Hukumar Hisbah, Muhammad Harun Ibn-Sina, ya ce sun fara sumamen ne domin haka aiyukan hukumar gada.
A cewar sa, sashe na 13(7) na dokar hana shisha ya tabbatar da cewa ta ana haramun a jihar Kano, inda ya jadda ƙudurin hukuma Hisbah na ci gaba da hana sha da sayar da ita a faɗin jihar.
Ya kuma jaddada ƙudurin hukumar wajen yaƙi da baɗala da kuma umarni da kyawawan aiyuka a jihar.