News
Gwamnatin tarayya ta gudanar da ayyukan tituna guda 21 a Kano – Fashola
Daga kabiru basiru fulatan
Ministan ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta gudanar da ayyukan tituna guda 21 a jihar Kano da kewaye, wanda ya kai kilomita 960.
A cewarsa, wasu daga cikin hanyoyin sun hada da babbar hanyar Kano zuwa Abuja, titin Kano zuwa Katsina da titin Kano zuwa Maiduguri da dai sauransu.
Da ya ke mayar da martani, Ganduje ya yabawa gwamnatin tarayya kan duk hanyoyin sadarwa a jihar da kewaye da ta gudanar.
A cewarsa, mambobin majalisar zartaswa na jihar suna da cikakkiyar masaniya game da kayayyakin more rayuwa da gwamnatin tarayya ta samar a jihar.
Ya ce, “Gwamnatin jihar ta na shirye-shiryen biyan diyya ga wasu hanyoyin, domin kaucewa cikas wajen kammala su. Gwamnatin tarayya ta farfado da hanyar Kano zuwa Maiduguri da Yobe zuwa Jigawa, wanda a baya an yi watsi da su shekaru da dama”. Ganduje.
Gwamna Ganduje, ya kuma mika godiyarsa ga gwamnatin tarayya kan aikin layin dogo a jihohi irin su Legas da Ibadan da kuma Kano.