Sports
Kasuwar ƴan ƙwallo: Everton ta tuntubi Lampard, Arsenal ta amince ta sayi wani sabon gola

Daga muhammad muhammad zahraddin
Everton za ta tattauna da Frank Lampard, da Vitor Pereira da kuma Duncan Ferguson a kan aikin kocinta.
Juventus ta amince ta sayi dan wasan gaban Fiorentina dan kasar Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 21, wanda ake alakanta shi da Arsenal, kan kudi fan miliyan 62.4. (Mail)
Porto ta ki amincewa da tayin fam miliyan 37 da Tottenham ta yi wa dan wasanta dan asalin Colombia Luis Diaz, mai shekara 25, wanda frashinsa ya kai fam miliyan 66. (Evening Standard)
Newcastle United ta kammala cinikin dan wasan tsakiyar Brazil Bruno Guimaraes mai shekara 24 daga Lyon kan fan miliyan 30. (Talksport) Kociyan Roma Jose Mourinho ya ci gaba da fatan kungiyar ta Serie A za ta iya sayen dan wasan tsakiya na Arsenal da Switzerland Granit Xhaka, mai shekara 29, kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa ta Janairu. (Mail)
Manyan ‘yan wasa biyun da West Ham ke zawarcinsu a kasuwar musayar ‘yan wasa a watan Janairu su ne dan wasan gaba na Albania Armando Broja, mai shekara 20, wanda ke zaman aro a Southampton daga Chelsea, da kuma dan wasan gaban Chile Ben Brereton Diaz, mai shekara 22, wanda ke taka leda a Blackburn Rovers. (Insider Food ball)
Everton da Leeds United da kuma Wolves suma suna sha’awar siyan Broja, wanda Southampton ke son ajiyewa fiye da kakar wasa ta yanzu. (Talk)
Aston Villa ta ki amincewa da tayin fan miliyan 30 da wata kungiyar kwallon kafa ta Premier ta yi wa dan wasan tsakiyar Brazil Douglas Luiz. Arsenal na tunanin zawarcin dan wasan mai shekaru 23 (Evening Standard)
Dole ne Arsenal ta jira har zuwa bazara, don samun ɗan wasa Cody Gakpo, mai shekara 22 yayin da PSV Eindhoven ta kulla yarjejeniya da Netherlands don tsawaita kwantiraginsa. (Mail
Arsenal ta amince da yarjejeniyar sayen golan Amurka Matt Turner, mai shekara 27, daga kungiyar New England Revolution ta Major League Soccer a bazara. (Mail)
Aston Villa da Everton da kuma Leicester City suna sa ido kan halin da dan wasan Ingila Jesse Lingard mai shekara 29 ke ciki. (Manchester Evening News)
Barcelona ta tuntubi Borussia Dortmund yayin da take neman dauko dan wasan bayan Belgium Thomas Meunier mai shekara 30 a matsayin aro daga Jamus. (Marca)
Ashley Young na Aston Villa, wanda zai iya taka leda a matsayin mai tsaron baya ko na gefe, ya ki komawa Newcastle United, dan kasar Ingila din mai shekara 36, yana son ci gaba da zama a Villa Park. (Mirror)