Connect with us

News

‘Yan sandan Ogun sun kama Fasto bisa laifin yin lalata da uwa da ‘ya’yan ta

Published

on

FB IMG 16433467719007257
Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

An kama wani Fasto mai suna Timothy Oluwatimilehin bisa zarginsa da kwana da wata mata da ‘ya’yanta mata biyu a Abeokuta, jihar Ogun.

‘Yan sanda sun ce Timothy yana limanci cocin Spirit-Filled International Christian Church a yankin Olumore na jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Abimbola Oyeyemi, ya ce kamen ya biyo bayan korafin da mijin da mahaifin wadanda abin ya shafa suka kai ofishin ‘yan sanda na Adatan.

Advertisement

Mijin matar ya ruwaito cewa limamin cocin nasu ya yaudari matarsa ​​da ’ya’yansa mata guda biyu, wanda ya dauke su a hannun sa yana kwana da su.

Bayan kama shi, Timothy ya amsa laifin aikatawa amma ya roki a gafarta masa.

Wanda ake zargin ya ce ya yi amfani da rashin fahimtar juna tsakanin matar da mijinta wajen aiwatar da wannan aika aika.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *