News
Hadaddiyar Daular Larabawa ta sassauta dokar hana shiga kasar ga ‘yan Najeriya daga ranar Asabar
Daga kabiru basiru fulatan
Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) za ta dawo da jigilar fasinjoji daga Najeriya da wasu kasashen Afirka 11 a ranar Asabar 29 ga watan Janairu.
Hukumar Rikici da Ba da Agajin Gaggawa ta Hadaddiyar Daular Larabawa (NCEMA) ta sanar da hakan a cikin wani sakon twitter ranar Laraba.
“Daga ranar 29 ga watan Janairu, an sake ba da izinin shiga UAE ga kasar Kenya, Tanzania, Habasha, Najeriya, Jamhuriyar Kongo, Jamhuriyar Afirka ta Kudu, Botswana, Eswatini, Lesotho, Mozambique, Namibia, da Zimbabwe,”