News
Ƴan sanda a Yobe sun kama soja bisa zargin fashi da makami
Daga
Kabiru basiru fulatan
Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Yobe ta kama mutum uku da zargi da fashi da makami da fasa gida domin sata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun yan sanda reshen Jihar Yobe ASP Dungus Abdulkarim ya fitar, cikin wadanda ake zargi har da wani soja da ke ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai.
Tunda farko mutanen uku dai sun fasa gidan wata mata a Sabon-Pegi da tsakar dare dauke da muggan makamai ciki har da bindiga ƙirar AK-47 inda suka sace kudi kimanin naira 250,000 haka kuma suka sace mota ƙirar Peugeot 307 da wayar salula Nokia.
Sai dai bayan ƴan sanda sun samu labarin wannan lamari, sai suka shiga aikin nemansu har suka kama su.
Tuni waɗanda ake zargin suka amsa laifukan da ake zarginsu da aikatawa.