News
Me ya sa Jamus ba ta son taimaka wa Ukraine da makamai a yakinta da Rasha?
Daga
Kabiru basiru fulatan
Sauran kawayen Ukraine na nuna mamaki da damuwa kan kin taimaka wa Ukraine da makamai da Jamus ta yi.
Amma wannan mataki na kasar mai karfi a Turai na da tarihi kuma yana da matukar mahimmanci a fahimci wannan dalilin.
A gabashin babban birnin kasar Berlin, akwai wasu manyan abubuwa na tayar da hankali da aka boye a wani filin da ake noman ciyawa.
Yayin da manoma ke aikin noma a filin sai suka rika cin karo da kasusuwan mutane, makamai da kuma wasu abubuwa da aka yi amfani da su a yakin duniya na II.
A 1945, tsohon shugaban kama karyar Jamus, Adolf Hitler ya ɓuya a wani gini da ke cikin kasa a Berlin.
Sojojinsa na ficewa, yayin da sojojin Tarayyar Soviet ke kara kutsawa zuwa gabashi, sai dai a lokacin sojojin Nazi sun tsaya cak domin ba shi kariya a kan wani tudu da ake kira Seelo Heights.