Connect with us

News

Ana kama matasa bisa zargin kashe mace don yin tsafi da ita a Ogun

Published

on

FB IMG 16434668611032951
Spread the love

Daaga

muhammad muhammad zahraddin

‘Yan sanda a jihar Ogun da ke kudancin Najeriya sun kama wasu matasa uku da ake zargi da kashe wata mace domin yin tsafi da ita.

Advertisement

Kakakin ‘yan sanda na jihar Abimola Oyeyemi ne ya tabbatar da kama wadanda ake zargi a Abeokuta.

Ya ce wadanda ake zargi ‘yan shekara 17 ne zuwa 20, an kuma kama su ne da safiyar ranar 29 ga watan Janairu biyo bayan koken da aka shigar hedikwatar ‘yan sanda da ke yankin Adatan a babban birnin jihar.

Shugaban kauyen da suka fito ya ce, an ga matasan na kona wasu abubuwa da suka yi kama da kan mutum a wajen wata shara a garin.

Advertisement

“Biyo bayan bayanin da muka samu, Abiodun Salau da ke jagorantar ofishin Adatan ya ja gaba aka kamo wadan nan matasa, na hudun kuma wanda saurayin matashiyar ne ya tsere,” in ji Oyeyemi.

Ya kuma kara da cewa bayan tambayoyi da aka yi wa wadanda ake zargi, sun amsa cewa abin da suke konawa kan matashiyar nan ce da saurayinta kuma abokinsu ya tsere.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *