News
Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram da mayakan ISWAP da dama a Yobe
Daga muhammad muhammad zahraddin
Rundunar sojin Najeriya ta ce a ci gaba da yaki da take da ” ‘yan ta’adda” a yankin arewa maso yammacin Najeriya, dakarun bataliya ta 120 da hadin gwiwar JTF sun kashe yan Boko Haram da mayakan ISWAP masu yawa da safiyar yau, a wani harin kwantan bauna da suka yi musu a kauyen Ngirbua da ke jihar Yobe.
A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukanta na sa da zumunta, rundunar ta ce dakarunta sun kashe mayaka da dama tare da kwace makamansu, amma sauran bayani kan abin da ya faru zai zo daga baya.