Sports
Kasuwar ƴan ƙwallo: Barcelona da Juve sun tuntuɓi Arsenal kan Aubamayeng, makomar Ramsey da Sterling
Daga muhammad muhammad zahraddin
Barcelona da Juventus sun mika wa Arsenal tayin daukar dan wasan gaban Gabon, Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 32 a matsayin aro na tsawon kakar wasa ta bana. (Athletic)
Kocin West Ham David Moyes na son sayen dan wasan gaban Leeds United Raphinha mai shekara 25 kafin a rufe kasuwar musayar ‘yan wasa ta Janairu. (Mirror)
Dan wasan Ingila Raheem Sterling na shirin komawa tattaunawa da Manchester City. Kwantiragin dan wasan mai shekaru 27 zai kare ne a bazarar 2023 kuma Barcelona, da Paris St-Germain da Real Madrid suna ci gaba da zawarcin dan wasan. (ESPN)
Ana sa ran Newcastle United za ta kara zawarcin dan wasan baya na Brighton dan kasar Ingila Dan Burn, mai shekara 29, sannan kuma suna sha’awar sayen dan kasarsu Eddie Nketiah, mai shekara 22, daga Arsenal. Kwantiragin dan wasan Nketiah zai kare a bazara. (Guardian)
Da alama dan wasan Wales Aaron Ramsey zai ci gaba da zama a Juventus bayan dan wasan tsakiyar mai shekara 31 ya ki amincewa da komawa Aston Villa, da Burnley, da Crystal Palace, da Newcastle United da Wolves a wannan watan. (Calciomercato)
Brentford na shirin sanar da daukar dan wasan Denmark Christian Eriksen a karshen mako. (Times)
Everton na sha’awar sayen dan wasan tsakiyar Ingila, Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 26 daga Chelsea. (Mail)
West Ham na tattaunawa da Reims kan cinikin dan wasan Faransa Hugo Ekitike mai shekaru 19, wanda kuma ake alakanta shi da Brentford, Brighton da Newcastle United. (Sky Sports)
Har ila yau Hammers din na ci gaba da tattaunawa da Marseille yayin da suke kokarin sayen dan wasan bayan Croatia Duje Caleta-Car, mai shekara 25, da dan wasan Senegal Bamba Dieng, mai shekara 21, a matsayin aro daga kulob din na Faransa. (90mints)
Juventus ta ki amincewa da tayin £20.8m da Aston Villa ta yi kan kan dan wasan Uruguay Rodrigo Bentancur, mai shekara 24. (Guardian)
Juventus na duba yiwuwar zawarcin dan wasan tsakiyar Italiya Jorginho mai shekara 30 a bazara, wanda kwantiraginsa zai kare a Chelsea a shekarar 2023. (Gazzetta dello Sport)
Monaco na son siyan dan wasan tsakiyar Faransa Aurelien Tchouameni, mai shekara 22, mai shekara 22, wanda Real Madrid ke nema, kuma ana alakanta shi da Chelsea da Manchester United. (Marca)