News
An lallashi Sergio Mattarella ya ƙara karɓar shugabancin Italiya zango na biyu duk da ba ya so
Daga kabiru basiru fulatan
Majalisar dokokin Italiya ta sake zaɓar shugaba Sergio Mattarella a zangon mulki na biyu.
Sai da a ka kai gwauro, a ka kai mari sannan a ka iya shawo kan Mattarella ya yarda da ci gaba da shugabacin ƙasar.
Shugaban, mai shekaru 80 da haihuwa, wanda ake mutuntawa sosai a ƙasar, ya sha nanata cewa ba shi da sha’awar komawa mulki a zango na biyu.
Sai dai daga baya, an samu nasarar lallasshin sa don ya ci gaba da zama bayan da ‘yan majalisar su ka kasa cimma matsaya kan wanda zai maye gurbinsa, bayan kai wa har zagaye na bakwai a zaɓe.
-
News3 days agoWasu Ƴan Daba Sun Kai Farmaki Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Center Dake Kano
-
News5 days agoWasu Fusatattun Matasa Sun Ƙona Mutum Uku Har lahira A Filato
-
News5 days agoAbin Takaici Ne A Kyale Mata Su Cire Wandunan Da Aka Basu Akan Titi Suna Dagawa A Cikin Al’ummar Da Ke Alfahari Da Kunya Da Addini
