Connect with us

News

Gwamnan Borno ya amince a bai wa wani asibiti mai zaman kansa kyautar naira miliyan 50

Published

on

FB IMG 16435601691998285
Spread the love

Daga Yasir sani abdullahi

 

Gwamnan jihar Borno da ke arewacin Najeriya Babagana Umara Zulum ya amince a bai wa wani asibiti mai zaman kansa a Maiduguri tallafin kudi da suka kai naira miliyan 50 da motar asibiti da magunguna da dai wasu sauran kayayyakin amfani a asibiti.

ISa Gusau
ISa Gusau

Ya yi hakan ne a wani mataki na ganin an karfafa bangaren lafiya na kasar domin inganta lafiyar jama’ar jihar ta Borno.

Gwamnan ya sanar da ba da tallafin ne lokacin da ya kai wata ziyara ta musamman asibitin da ke yankin Abbaganaram.

Advertisement
ISa Gusau

Asibiotin dai na wata al’umma ne, wanda wani dan kasuwa a Maiduguri ya gina, wanda ya rasu kwanan nan, gwamnan ya nemi asibitin da ya dauki likitoci biyu da kuma malaman jinya hudu, su kuma karfafa ma’aikatansu, ita kuma gwamnatin Borno za ta rika biyan salarin sauran ma’aikata shidan da ta nemi asibitin ya dauka aiki.

Gwamnan kuma ya yi ta’aziyya ga iyalan dan kasuwar da ya fara samar da wannan asibiti, Tijjani Bolori wanda ya nuna damuwa kan rayuwar mutane lokacin da yake raye.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *