Connect with us

News

Bagudu ya saki N220m don gina masallaci a Kebbi

Published

on

FB IMG 16435443570408627
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

 

Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya ce gwamnatin jihar ta saki Naira miliyan 220 domin gina masallaci, da za a laƙanawa suna Sarki Muhammadu Bello a garin Koko da ke Ƙaramar Hukumar Koko Besse a jihar.

Advertisement

Gwamnan ya baiyana hakan ne a ranar Asabar a lokacin da yake jawabi a wajen bikin aza tubalin ginin a garin Koko.

Bagudu ya ce: “Gamu nan a yau Asabar, 29 ga watan Janairu, domin aza tubalin ginin sabon masallaci a garin Koko, Masallacin Sarki Muhammadu Bello.

“Gwamnati ta amince da gina masallacin kuma tuni an riga an fitar da Naira miliyan 220 domin gudanar da aikin, daga farko har zuwa a kammala shi.”

Advertisement

Bagudu, wanda kuma shi ne Shugaban ƙungiyar Gwamnonin APC, ya shaida wa ɗaruruwan jama’ar da su ka yi dandazo domin shaida bikin mai dimbin tarihi.

Ya sanar da cewa, gwamnatin jihar ta kuma amince da gina sabuwar kasuwa daura da masallacin domin bunƙasa kasuwanci da cinikaiya a yankin.

Bagudu ya ƙara da cewa an kuma amince da Naira miliyan 314 domin gina sabuwar kasuwar.

Advertisement

A cewar gwamnan, zaunar da kasuwar a wani wuri, an yi nufin rage cunkoso a kewayen kasuwar ta yanzu, da share fagen zirga-zirgar ababen hawa, da kuma jama’a.

Ya yi addu’ar Allah ya sa a kammala ayyukan cikin nasara a kan lokaci don amfanin bil’adama.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *