News
Hisbah ta sassauta dokar hana amfani da mutum-mutumi, inda ta ce teloli za su iya amfani da gunki maras kai
Daga kabiru basiru fulatan
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta jaddada cewa dokar haramta amfani da mutum-mutumi a shagunan teloli da na sayar da tufafi na nan daram a faɗin jihar.
Sai dai kuma hukumar ta yi sassauci, inda ta bada umarnin amfani da mutum-mutumi amma wanda a ka ƙera shi ba tare da kai ba.
A wata sanarwa da Hisbah ta wallafa a shafinta na Facebook da harshen Hausa, Hukumar ta ce ta dogara ne da dokar Kano ta haramta munanan aiyuka ta 2003 da a ka yi wa kwaskwarima domin aiwatar da hana amfani da mutum-mutumin.
“An haramta duk wani mutum-mutumi na jinsin maza ko mata a Kano. Waɗanda aka yarda a yi amfani da su su ne waɗanda babu kai, sai iya gangar jiki kawai,” in ji sanarwar.
A cewar sanarwar, Babban Kwamandan kwamandan Hisbah na Kano, Haruna Ibn-Sina, shi ya baiyana hakan a wata ganawa da ƙungiyar teloli ta ƙasa, reshen Jihar Kano a ranar Alhamis, 27 ga watan Janairu.
“Sannan kuma Babban Kwamandan ya sake shirya wani taro da ƙungiyoyin teloli kan yadda za su riƙa amfani da mutum-mutumi wajen tallata hajojin su.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Yanzu ƙungiyar ta Hisbah za ta shirya taron wayar da kan teloli kafin jami’anta su fara aiwatar da sintirin hana dokar.”