News
EFCC ta tsare Darakta-Janar na VON, Osita Okechukwu, bisa zargin almundahanar N1.3bn

Daga Yasir sani abdullahi
Hukumar Yaƙi da Masu yi wa Tattalin Arzikin ƙasa Zagon-ƙasa, EFCC, ta tsare Darakta-Janar na gidan rediyon ƙasa, Voice Of Nigeria, VON, Osita Okechukwu.
Wata majiya da ke kusa da hukumar ta baiyana cewa an tsare Okechukwu ne bisa zargin haɗin-baki, ɓata sunan ofishi da kuma almubazzaranci da dukiyar al’umma da su ka kai Naira biliyan 1.3.
Majiyar ta ƙara da cewa Darakta-Janar ɗin ya isa shelkwatar EFCC da ke Abuja da misalin karfe 1:30 na rana domin amsa gaiyatar da ta yi masa.
Majiyar ta baiyana cewa har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, Okechukwu yana hannun hukumar EFCC.
“Har yanzu yana tare da jami’an EFCC.”
Da aka tuntubi mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya tabbatar da gaiyatar shugaban VON ɗin, amma bai ƙara cewa komai ba bayan wannan.