Connect with us

News

Amurka da Rasha sun yi kaca-kaca a wajen taron MDD kan Ukraine

Published

on

123066933 073443964 1.jpg
Spread the love
  1. Daga
  2. muhammad muhammad zahraddin
  3. An yi faɗa kaca-kaca tsakanin jakadun Amurka da Rasha a wajen taron Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan da Amurka ta kira wani taro don tattanawa kan yadda Rasha ke girke dakaru a kan iyakarta da Ukraine.

Jakadiyar Amurka Linda Thomas-Greenfield ta ce aikin girke dakarun na Rasha shi ne irinsa mafi girma da aka taɓa gani a yankin Turai cikin gwamman shekaru.

Takwaranta na Rasha ya zargi Amurka da haifar da ruɗani da kuma yin shisshigi a al’amuran Rasha.

Amurka da Birtaniya sun yi alkawarin ƙara ƙaƙaba wa Rasha takunkumai idan har Rasha ta kutsa Ukraine.

Sakatariyar Harkokin Wajen Birtaniya Liz Truss ta ce ana tsara dokokin da za su mayar da hankali kan mutane da kuma harkokin kasuwanci da dama a Rasha fiye da waɗanda ake da su a yanzu.

Advertisement

Wani jami’in Amurka ya ce takunkuman da Fadar Washington za ta sanya na nufin za a cire mutanen da ke da kusanci da gwamnatin Rasha daga tsarin hada-hadar kasuwanci na duniya.

A ƙiyasi Rasha ta girke dakaru 100,000 da tankokin yaƙi da igwa-igwa da makamai masu linzami a kusa da kan iyakar Ukraine.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *