News
Kamfanin jirgin sama na Ethiopia ya dawo safara da jirgin Boeing 737 Max bayan hadarin 2019.
Daga
muhammad muhammad zahraddin
Kamfanin sufurin jirgin sama na Ethiopia ya dawo safara da jirgin Boeing samfurin 737 Max a karon farko tun bayan hadarin da ya yi a shekarar 2019.
Duka mutun 157 da ke cikin jirgin sun mutu, jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin sama na Addis Ababa, inda zai je babban birnin kasar Kenya Nairobi.
Jirgin yana dauke da fasinjoji 149 da ma’aikata takwas, fasinjoji 32 ‘yan kasar Kenya ne, sai 18 ‘yan Kanada da takwas ‘yan Amurka sai kuma bakwai ‘yan Birtaniya.
Kuma watanni biyar kafin nan samfurin 737 Max ya fadi a Indonesia, inda ya kashe dukkanin mutun 198 da ke cikinsa.
Jirgin na farko da ya tashi a yau ya dauki tawagar shugaban kamfanin da manyan jami’ansa da shugabannin kamfanin kera jirgin na Boeing da ministoci da jakadu da jami’an gwamnati da ‘yan jarida da sauran fasinja.
To amma a yanzu Kamfanin Ethiopian Airline ya ce ya gamsu da irin gwaje-gwajen da kasashen Turai da Amurka da China suka yi wa jirgin kafin ya dawo aiki a kasashensu.
Hukumar kamfanin ta kuma ce akwai wasu kamfanonin sufurin jirgin sama 35 da suka koma aiki da shi.