News
Zan nemi takarar shugaban kasa idan har PDP ta ba Kudu tikiti – Peter Obi

Daga
muhammad muhammad zahraddin
Tsohon gwamnar Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya, Peter Obi, ya ce zai tsaya takarar shugabancin kasar idan har jam’iyyarsa ta PDP ta bai wa kudu tikitin.
Mista Obi, wanda ya yi wa PDP takarar mataimakin shugaban kasa a 2019, tare da Atiku Abubakar, ya bayyana hakan ne a sakon da ya wallafa a tuwita ranar Talata.
“Eh tabbas zan tsaya takarar shugabancin Najeriya domin samun damar yi wa kasata hidima a matsayin shugaban kasa, idan har jam’iyyata ta PDP ta kai tikitin kudu, amma ko an bayar da dama ga kowane bangare na kasar,
‘Yan Najeriya za su ji daga gareni,” ya rubuta a shafin Tuwita.
Sanarwar Mista Obi na zuwa ne kasa da awa 24 bayan da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya shelanta aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasar karkashin jam’iyyar PDP.