Connect with us

News

Yadda ‘yan sanda suka ceto yara sama da dari a gidan mari a Kano

Published

on

123069988 6e55f5d6 b9bf 440c 99de 2b2237510a52.jpg
Spread the love

DAGA 

muhammad muhammad zahraddin

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto yara sama da dari daya da take zargin ana azabtar da su a wani gidan mari da ke birnin Kano.

Advertisement

‘Yan sandan sun ce sun ceto yaran ne da shekarunsu suka kama daga 4 zuwa 10, bayan sun sami koke daga wasu daga cikin daliban makarantar da suka gudu lokacin da aka tafi binne daya daga cikinsu da suke zargi dan mai makaranatar ne ya yi sanadiyar mutuwarsa ta hanyar azabtarwa da duka.

A hirarsa da INDARANKA, kakakin rundunar ‘yan sandan na Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce: ”Wasu matasa ne su goma wadanda shekarunsu suke tsakanin 10 zuwa 14 suka je hedikwatar ‘yan sanda inda suka shigar da korafi a kan wani mutum da yake gudanar da makarantar mari ba bisa ka’ida ba, wadda daga can suka gudo, mutumin mai suna Musa Safiyanu dan kimanin shekara 55 da ke unguwar Na’ibawa ‘yan-lemo, karamar hukumar Kumbotso a nan Kano.”

Ya kara da cewa: ”Sun ce a wannan gida nasa akwai yara sama da dari wasu an daure su wasu kuma an kulle su a dakuna wanda da daya ya yi laifi aka dinga dukansa, dan gidan mai gudanar da makarantar shi ya yi dukan wanda dukan yayi sanadiyyar mutuwar daya daga cikinsu.”

Advertisement

SP Kiyawa ya ce yaran da aka samu a makarantar su 113 ne, inda aka tarar da su a yanayi na azabtarwa da rashin kyawun wurin kwana da abinci, sannan ba abincin da ake ba su sai tuwo safe da rana.

”Hakazalika ruwa daya suke sha a cikin ban-daki da yake fitowa, wannan ruwa ake sha wannan ruwa ake komai da komai da shi,” in ji kakakin.

”Ban da ma wasu cin zarafin na neman maza kananan yara,” a cewar SP Kiyawa.

Advertisement

Yanzu dai gwamnatin jihar Kano, wadda ta rufe makarantar, ta ce lalle sai ta gurfanar da mai makarantar a kotu, bisa laifukan da ake zarginsa da su, kamar yadda Kwamishinan Addinai na jihar, Muhammad Tahar Adamu da ake wa lakabi da ”Baba Impossible” ya bayyana wa INDARANKA

Ya kara da cewa: ”Idan ta kama ma sai an biciko gawar nana an fito da ita daga kabari an kai ta an yi bincike a kanta don a tabbatar da sanadiyyar kisan.”

Kwamishinan ya kuma ce yaran da aka kwashe suna hannun hukuma za a nemo iyayensu, ”ragowar yara wajen 170 suna can ”rimand home” wajen ajiye yara kangararru za a bai wa iyayensu.”

Advertisement

Ya kara da cewa, “su iyayen idan sun zo wanda duk ya bada dansa dan karami irin wannan dan shekara hudu, biyar, shida babu shakka shi ma sai mun tuhume shi da abin da ake kiransa wulakanta yara, za mu caje shi, shi ma ba za mu bari su tafi haka ba.”

Kwamishinan ya kuma ce gwamnati tana nan tana tsara yadda za ta yi gidajen marin ta ba su dokoki.

Ya ce an gayyato ‘yan sanda da ma’aikatan lafiya, sun duba tsarin kuma za a samar da hatta ‘yan kwana-kwana ta yadda za a tabbatar gidajen sun dace.

Advertisement

Waiwaye

Tun bayan da gwamnatin Najeriya, ta haramta tafiyar da gidajen mari a kasar, wannan shi ne karo na biyu da aka samu irin wannan gida na mari a jihar Kano, sai dai wannan shi ne wanda aka fi samun yara masu karancin shekaru masu yawa a cikinsa.

Gidajen mari ko horo kamar yadda wasu suka fi daukarsu, iyaye ko ‘yan uwa kan kai yaron da ake ganin yana neman kangarewa da nufin ladabtar da shi.

Advertisement

Sai dai tun a wanchan lokacin akwai zarge zarge na cin zarafi a gidajen.

A sakamakon zarge-zargen a 2019, gwamnatin jihar ta bayar da umarnin rufe daukacin gidajen mari da ke Jihar, har zuwa lokacin da za ta fitar da tsarin da ya dace.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *