News
Majalisar Dokoki ta Kano ta sahale gina gidaje 5,000
Daga
Kabiru basiru fulatan
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sahale gina gidaje 5,000 domin ma’aikatan gwamnati da malaman makaranta.
Kakakin Majalisar, Hamisu Ibrahim Chidari ne ya baiyana hakan a jiya Litinin a wata wasiƙa da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya aikewa majalisar don neman ta sahale masa ya aiwatar da aikin gina gidajen a Ƙananan Hukumomi 44 na jihar.
Bayan da Majalisar ta tattauna a kan ƙudurin na gwamnan, da ga ƙarshe sai duka ƴan majalisar su ka amince da aiwatar da aikin ginin.
Da ya ke karanta wasiƙar, Chidari ya ce za a aiwatar da aikin ne a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar kula da Dokokin Aiyuka da Aiwatarwa ta Jiha, Rabi’u Suleman Bichi.