News
Sifeto-Janar ya naɗa mace ta farko a matsayin mai bada shawara ga rundunar tsaron haɗaka ta ƙasa-da-ƙasa
Daga kabiru basiru fulatan
Sifeto-Janar na Ƴan Sanda, Usman Alƙali Baba ya naɗa Amabua Ashe Mohammed a matsayin mace ta farko Mai bada Shawara ga Rundunar Tsaron Haɗaka ta Ƙasa-da-ƙasa, MNJTF a N’Djamena, Chadi.
Kakakin rundunar na ƙasa, Frank Mba ne ya sanar da naɗin a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Abuja.
Sanarwar ta ƙara da cewa, Mohammed, wacce ita ce Mataimakiyar Kwamishinan Ƴan Sanda, ACP, ta zama ƴar sanda ta farko a tarihi da ta riƙe muƙamin mai wahala na gudanar da ayyukan ‘yan sanda.
Mba ya ƙara da cewa naɗin Mohammed shaida ce ta ayyuka da gudumawar da jami’an rundunar suke bayarwa wajen yaƙi da ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma a Nijeriya da ma duniya baki daya.
Sanarwar ta ce a sabon muƙamin na Mohammed, za ta riƙa tabbatar da biyayya da ƙwarewa wajen gudanar da aiki.
Sannan, in ji sanarwar, za ta riƙa bada shawarwari a kan hanyoyin samar da zaman lafiya wajen yaƙi da Boko Haram da Rundunar Tsaron Haɗaka ta Ƙasa-da-ƙasa ke yi.
Sanarwar ta ƙara da cewa Mohammed ta samu yabo wajen gagarumar ƙwarewa wajen kokarin samar da zaman lafiya tsakanin ƙasashe, inda ta yi aiki a yunƙurin samar da zaman lafiya na ƙasashe tsawon sama da shekaru ashirin.
Sanarwar ta ce bayan da Sifeto-Janar ɗin ya taya ta murna bisa sabon muƙamin nata, ya kuma hore ta da ta yi amfani ɗumbin ƙwarewar ta wajen tafiyar da ƙudurin samar da zaman lafiya da MNJTF ta ke yi.