News
ASUU ta aiyana Litinin a matsayin ranar hutun karatu a BUK
Daga yasir sani abdullahi
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, ASUU reshen Jami’ar Bayero, ta aiyana ranar Litinin 7, ga Febrairu a matsayin ranar da ba za a gudanar da al’amuran karatu a jami’ar ba.
Ƙungiyar ta sanar da hakan ne a wata sanarwa da shugaban ƙungiyar, Kwamared Haruna Musa da sakatarensa,Yusuf Madugu su ka sanyawa hannu a jiya Alhamis.
A sanarwar, ASUU ta ce a maimakon rashin gudanar da harkokin karatu da za ta yi a ranar, za ta yi amfani da damar wajen wayarwada kan ɗalibai irin halin da gwamnatin taraiya ta jefa su a ciki na ƙin biyansu haƙƙoƙinsu.
A cewarsu, har yanzu gwamnatin tarayya ta ki cika alkawuran da ta daukar musu, duk da cewa an lallabasu da hana su tafiya yajin aiki.
Idan za a iya tunawa dai tun a watan Disambar bara ne kungiyar ta ASUU ta yi yunkurin tafiya yajin aiki amma aka lallabasu suka hakura, bisa alkawarin za a biya musu bukatunsu.
Sai dai a cewar kungiyar tun bayan da aka lallabasun har yanzu gwanatin taki sauraron su ballantana ta cika alkawuran da ta dauka.
A don hakan ne kungiyar taga dacewar ta tattauna da dalibai da sauran masu ruwa da tsaki musamman iyayen yara wajen sanar da su halin da ake ciki.
Haka kuma tana fatan iyayen yaran da daliban ba za su zargesu ba da zarar sun yi yunkuri komawa yajin aikin.