News
Barayin daji sun kashe ALH. JAFARU RABI’U dagacin garin Yangayya dake jihar Katsina
Barayin daji sun kashe ALH. JAFARU RABI’U dagacin garin Yangayya dake jihar Katsina
Mazauna garin sun shaidawa manema labarai cewa, barayin dajin wadanda yawansu ya kai 200 sun zo garin ne akan babura inda suka harbin kan mai uwa da wabi.
Rahotanni sun ce yan bindigar sun kuma kashe wasu mutane 4 wadanda suka yi kokarin tserewa lokacin da ‘yan bindigar suka shigo garin.
Shidai garin Yangayya yana yankin Karamar hukumar Jibia ne a jihar ta Katsina