News
Mataimakin shugaban kasa ya karbi bakuncin tsohon mataimakin Ganduje
Daga kabiru basiru fulatan
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano a zangon mulkin farko na gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Farfesa Hafiz Abubakar, ya ziyarci mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, a fadar mulki ta Villa, yayin da sukayi wani gani a tsakaninsu.
Ziyarar na zuwa ne kasa da makonni biyu da wata kungiya da nada Farfesa Hafiz Abubakar a matsayin shugaban yakin neman zaben Yemi Osinbajo na kasa baki daya, a muradinsu na ganin ya samu tikitin takarar shugaban kasa a kakar zaben shekarar 2023 cikin jam’iyyar APC, domin ya gaji buzun shugaba Muhammadu Buhari.
Shin kuna ganin idan Osinbajo ya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, zai iya dakko Farfesa Hafizu a matsayin dan takarar mataimaki?
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
