News
Buhari Ya Waiwayi Direban Da Ya Kai Shi Gida Bayan An Kai Masa Hari A 2014
Daga
muhammad muhammad zahraddin
Mutumin da ya kai Shugaba Muhammadu Buhari gida a lokacin da aka kai masa hari a shekara ta 2014 a Kawo da ke Jihar Kaduna ya samu kyautar mota da kudi. Umar Isa wanda aka fi sani da Umar Isa Small Fire da ke zaune a Tudun Wadan Zariya kuma mai sana’ar tukin mota ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru da kuma abin da ya biyo baya a wannan lokaci.
Ya ce a wancan lokaci ya dauki fasinja zuwa Kaduna daga Zariya ne, isarsu Kawo ke da wuya sai suka ji kara mai karfi.
Ko da ya wai ga duk fasinjojinsa sun yi ta kansu daga nan sai ya kalli gabansa sai ya ga mutum daya a tsakiyar hanya a tsaye sai ya nufi inda yake sai wasu ’yan sanda suka daga bindiga suka ce ya tsaya.
Ya ci gaba da bayanin cewa isarsa ke da wuya sai ya ga ashe Shugaba Muhammadu Buhari ne sai ya bude masa mota ya shiga saboda motarsa bam ya yi kaca-kaca da tayoyinta.
Ya ce da suka isa gidan Buhari, “wani mutum mai farin gashi ya fito ya tambaye ni ‘kai ne ka kawo shi gida’? na ce eh, sai ya ce in gyara motar in dan jira.
Shi wannan mutumin ya zo ya ba ni Naira dubu biyu muka yi sallama na bar su.”
Umar Isa ya ce, “Jama’a sun ta yin maganganu da shawarwari in yi kokarin yadda zan ga Shugaba Muhammadu Buhari tun da ya zama Shugaban Kasa, amma Allah bai yi ba sai yanzu ta dalilin ziyarar aiki da ya kawo Zariya. Akwai wani dan uwana mai suna Nasiru Aliyu Babanyaya wanda ya bukaci da mu yi hira ya sanya a kafar sadarwa ta zamani ko Allah Ya sa Shugaba Muhammadu Buhari ya gani. Na yarda muka tattauna da shi kuma ya saka bayan kwana uku da saka wannann hira sai aka kira ni zuwa ofishin DSS aka ba ni buhu 10 na shinkafa da man gyada da man ja da kuma katan 10 na taliya da kuma kudi Naira dubu 200.
Bayan kwanaki kadan kuma sai Nasiru Aliyu Babanyaya ya kira ni daidai lokacin Sallar La’asar ya ce na yi baki a kofar gidana.”
Umar Isa ya ce isarsa gida ke da wuya muka shiga Masallaci muka yi sallah, sai suka ce ga mota in ji Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da kudi Naira 700,000.
“Ban taba rike kudi nawa na kaina ba da suka wuce Naira dubu goma ba a rayuwata kuma ina da mata biyu da yara 12. Don haka, rayuwata da ta iyalina ta canza.”