News
Gwamna Zulum ya kaddamar da raba motocin haya guda 610 da babura masu kafa uku da mota bas a Maiduguri.

Gwamna Zulum ya kaddamar da raba motocin haya guda 610 da babura masu kafa uku da mota bas a Maiduguri.
Ya bada tallafin kudi Miliyan 50 ga masu aiki su dubu 1,000.
Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da motocin haya guda 610, babura masu kafa uku da bas don inganta zirga-zirgar jama’a a cikin birane a Maiduguri da wasu sassan kananan hukumomin Jere da Konduga da ke karkashin babban birni.