Daga
muhammad muhammad zahraddin
Wakilin Masar a Kamaru Medhat El-Meligy, ya ce Masar za ta ware jiragen sama 10 domin daukar magoya bayan kasar zuwa Kamaru lokacin da za a buga wasan karshe na gasar Afcon, wanda za a yi a ranar Lahadi mai zuwa.
El-Meligy ya kara da cewa adadin magoya bayan Masar zai iya kai wa 3,000, wadanda za su je kasar.
Za a buga wasan karshen na Afcon tsakanin Masar da Senegal a yammacin Lahadi a filin wasa na Olembe da ke Yaounde.
Masar ta samu damar zuwa wasan karshe ne bayan bugun fenariti da aka yi wanda Kamaru ta ci daya tal cikin wadanda ta buga.
kungiyar Pharaohs za su wasan ne ba tare da kocinsu ba, Carlos Queiroz, wanda aka bai wa jankati a wasansu da Kamaru.