A yau Lahadi Masar za ta kara da Senegal a wasan ƙarshe na gasar cin kofin Afrika wato Afcon da Kamaru ke karɓar baƙunci.
Wasa ne mai zafi ganin cewa taurarin ƙungiyar Liverpool Mohamed Salah da Sadio Mane za su kara a wasan inda Salah zai buga wa Masar sai kuma Mane ya buga wa Senegal.
Sau bakwai Masar na zama zakara a gasar ta Afcon, inda Senegal kuma a karon farko take so ta ɗauki wannan kofi.
Senegal ta je wasan ƙarshe a gasar ta Afcon a shekarun 2002 da kuma 2019 inda duka ta yi rashin nasara.
Ita kuma Masar rabonta da ta ɗaga wannan kofi na Afcon tun a 2010.
A halin yanzu dai Kamaru mai masaukin baƙi ce ta zo ta uku a gasar bayan ta yi waje da Burkina Faso a jiya Asabar.