Connect with us

Sports

Afcon 2021 Senegal ta lashe gasar cin kofin Afrika ta Farko a tarihi

Published

on

Spread the love

Daga muhammad muhammad zahraddin

Ƙasar Senegal ta lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Afrika Acon ta shekarar 2021

An shafe mintuna 120 ana fafatawa ba tare da an samu wanda ya ci a fili ba, har sai da aka kai bugun daga kai sai mai tsaron gida

Advertisement

A nan ne Senegal ta doke Masar da ci 4 da 2.

An fara gasar ne da ƙungiyoyi 24, kafin a gangaro zuwa ƙasashe biyu da suka buga wasan ƙarshen a yanzu.

Masar ta rasa damarta ta ɗaukar kofin karo na 8, inda ita kuma Senegal ta ɗauki kofin a karon farko

Advertisement

Tun a zagayen farko Sadio Mane, wanda aka zuba wa ido a kansa a ɓangaren ƴan wasan Liverpool ya kasa cin bugun daga kai sai mai tsaron gida da ƙasarsa ta samu, wani abu da ya rage ƙarin guiwar ƴan wasan da farko.

Golan Masar Gabaski ya yi namijin ƙoƙari ta hanyar ture ƙwallaye da dama da aka riƙa buga masa, ciki har da ture ƙwallo ɗaya a bugun daga kai sai mai tsaron gida, abun da ya sa aka ba shi golan da ya fi taka rawa a wasa.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *