Shugaban Senegal Macky Sall ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutun aiki don ci gaba da murnar lashe Kofin Ƙasashen Afirka (Afcon 2021) da tawagar ƙasar ta yi ranar Lahadi da dare a Kamaru.
Shugaban wanda yanzu ba ya cikin ƙasar, ya soke taƙaita balaguron da yake yi domin tarɓar taurarin ‘yan wasa nasa.
Shugaba Sall zai bai wa tawagar kyauta ta musamman ranar talata a fadarsa, a cewar kafar yaɗa labaran ƙasar ta RTS.
Senegal ta lashe kofin Afcon a karon farko a tarihi bayan ta buga wasan ƙarshe har sau biyu a baya – a 2019 da 2022.
Sun doke tawagar Egypt ne mai Mohamed Salah 4-2 a bugun finareti bayan an tashi wasa 0-0.