Connect with us

News

Rikicin APC a Kano: Za mu bi umarnin Allah da na Jam’iya mu yarda da sulhu — Shekarau

Published

on

FB IMG 16441710279693944
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

 

Jagoran ɓangaren da ke rikicin shugabancin jam’iyar APC a Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce za su bi umarnin Allah da kuma na uwar jam’iya su sulhunta da tsagin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar

Advertisement

Jaridar indaranka ta rawaito cewa, a ci gaba da zaman sulhu tsakanin ɓangarorin biyu da su ke ta gabza rikicin mallakar jam’iyyar tun bayan kammala zaɓen shugabannin jam’iya, a jiya Asabar ne dai Kwamitin Riƙo na APC ya kira jagororin biyu da su je Abuja domin wata ganawa ta gaggawa.

Bayan tashi da ga taron gaggawar, ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe, jam’iyyar ta yanke shawarar tura wani kwamiti mai ƙarfi zuwa Kano domin tabbatar da an bi sabon tsarin rabon muƙaman jam’iyyar daidai.

A wata taƙaitacciyar sanarwa bayan taron na jiya Asabar da daddare, mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta samar da tsarin sanya kowa cikin harkokin jam’iyyar ta APC a Kano.

Advertisement

A cewar Sule, a gobe Litinin za a sanar da duk ɓangarori biyun halin da ake ciki.

A wani saƙon murya da Sule ya fitar ta kafar WhatsApp a yau Lahadi, Shekarau ya ce Allah Ya yi umarni da a yi sulhu, da kuma nuna alherin da a gurare da dama a cikin Alƙur’ani mai girma.

Bayan da ya janyo wasu ayoyi a surori uku da su ka yi horo da sulhu ga muminai, inda ya yi kira da ƴan jam’iyar APC a jihar da su bi umarnin Ubangiji su bada goyon baya a sulhun domin samun zaman lafiya a jam’iyar.

Advertisement

Shekarau ya kuma ƙara da cewa da shelkwatar jam’iya ta ƙasa ba ta karɓi sakamakon zaɓen shugabannin jam’iya na jiha ba, da ɓangaren na sa ba zai samu nasarar da ya samu a kotu ba.

“A halin yanzu, muna jiran wadannan ƙa’idoji da matakan sulhu da ga uwa jam’iya.

“Don haka mu na kira ga magoya baya da ƴan jam’iyar APC a jihar Kano da mu ƙara hakuri tare da addu’ar Allah Ya bamu mafita. Ina kuma jan hankalin masu iƙrarin cewa babu sulhu, su tuna cewa sulhu umarni ne da ga Allah Subhanahu wa Ta’ala.

Advertisement

“wajibi ne mu baiwa uwar jam’iyya haɗin kai ta re da kyautata musu zato wajen samar da sulhu wanda zai samar da adalci a cikin jam’iyar mu ta APC a dukkanin matakai a jihar Kano.

“Mu na roƙon Allah da Ya samar mana mafita mafi alheri,” in ji Shekarau.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *