News
Fashewar tukunyar gas ta kashe mutum 1 a kan hanyar kai kayan Katsina
Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum ɗaya sakamakon fashewar da rukunyar gas ta yi a hanyar zuwa Katsina.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Abdullahi ya fitar a Kano a yau Talata.
A cewarsa, haɗarin ya faru ne a ƙauyen Ijarawa da ke Ƙaramar Hukumar Bichi a Jihar Kano da misalin ƙarfe 7:46 na safe, inda ya ƙara da cewa mutum ɗaya ya tsira.
“Mun samu kiran gaggawa daga Sufeto Daiyabu Tukur da karfe 07:46 na safe cewa wata mota da ke dauke da tukwanen gas din girki ta fadi a kan hanya kuma daya daga ciki ta fashe.
“Bayan samun labarin, mun aika jami’an mu zuwa wajen da abin ya faru cikin gaggawa da misalin karfe 8:00 na safe domin ceto wadanda abin ya shafa,” in ji sanarwar.
Abdullahi ya yi bayani cewa motar ƙirar J5 ce mai lamba FB 52 LAD, wacce ta nufi Katsina daga Kano kuma tana jigilar iskar gas din girki ne.
Ya ƙara da cewa haɗarin ya rutsa da mutane biyu, Maikano Muhammad mai shekaru 45, wanda shi ne ya rasu, yayin da Abdullahi Usman, mai shekaru 40, a ka ceto shi da ransa.
“Dukkan wadanda abin ya shafa an mika su ga wani Usman Usman na ofishin ‘yan sanda dake Bichi.
“Ana binciken musabbabin lamarin,” in ji shi.
Jami’in hulda da jama’an ya yi kira ga direbobi da ke daukar tukwanen gas din da su kara taka-tsan-tsan da yin tuki cikin kulawa domin gujewa afkuwar haɗurra a titi.