Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 58 da suka kamu da cutar korona ranar Talata.
Jihohin da mutanen suka fito bakwai ne da suka haɗa da Legas (35) da Abuja babban birnin ƙasar (9) da Edo (5) da Delta (4).
Sauran su ne Kano (2) da Rivers (2) da Kaduna (1). Rahoton na NCDC ya nuna babu wanda cutar ta kashe a Talatar.
Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 253,833 ne suka harbu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta a Fabarairun 2020. Kazalika ta yi ajalin mutum 3,139.