News
Matsalar tsaro: ‘Yan bindiga sun jefa al’umma a garuruwan Zamfara da Katsina cikin halin ni-‘yasu
Daga kabiru basiru fulatan
Matsalar tsaro na ci gaba da tada hankula da daidaita al’umomi a yankunan arewacin Najeriya, baya ga mutanen da ke rasa rayuka ana kuma samun karin mutanen da ke gudun hijira.
Harin baya-bayanan da ya daidaita mutane da gidajensu shi ne wanda aka kai garuruwan Zamfara da Katsina a cikin wannan makon.
Ko a maraicen jiya Talata sai da ‘yan bindiga suka kai farmaki kauyen Hayin Dan Maciji na yankin karamar hukumar Gusau a Zamfara tare da hallaka mutane.
Sai dai yayin da ake cikin wannan yanayi su kuwa jama’ar garin garin Doma na jihar Katsina jajircewa suka yi, suka fatattaki wasu ‘yan bindiga da suka yi yunkurin kai masu hari.
Zuwa wayewar safiyar wannan Larabar mafi rinjayen jama’ar garin Hayin Dan Maciji na gundumar Ruwan Baure a yankin karamar hukumar Gusau, sun tsere zuwa wasu garuruwa makwabta.
Me wadanda suka tsira ke cewa?
Wani mutumin garin, wanda muka zanta da shi a kan hanyarsa ta gudun hijira, ya shaidawa BBC irin halin tashin hankalin da suka shiga:
”Muna cikin mawuyacin hali, da mu da iyalan mu da yara duk mun tarwatse, wasu ma ba su san inda ‘yan uwa da abokan arzikinsu su ke ba.