News
EFCC ta damƙe wani da ya damfari sirikin sa naira miliyan 3
Daga kabiru basiru fulatan
A jiya Laraba ne dai Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC, shiyyar Jihar Kaduna ta gurfanar da wani Yakubu Musa a gaban Babbar Kotu ta Kaduna, ƙarƙashin Alkali Darius Kobo bisa laifin damfara.
Wata sanarwa da kakakin EFCC ɗin, Wilson Owujaren ya fitar ta ce wanda a ke zargin, tun a wani lokaci a 2014, ya karɓewa wani mai suna Thalmon Friday kuɗi har Naira miliyan 3 domin ya dai masa fili a unguwar Mahuta a Kaduna, shine ya gudu da kuɗin dabo da shi wanda ya shigar da ƙara bai ga fili ba kuma ba a dawo masa da kuɗinsa ba.
Laifin ya saɓawa sashe na 308 na kundin dokokin laifuka ta Jihar Kaduna kuma laifin hukunci ne a karkashin sashe 309 na kundin dokokin.
Da a ka karanta masa laifukansa, wanda a ke zargin ya musanta.
Bayan ya musanta, sai lauyan mai ƙara, Maryma Lawan, ta roƙi kotu da ta sanya rana domin a fara shari’ar, inda lauyan wanda a ke ƙara Haruna Magaji ya roki kotun da ta baiwa wanda a ke zargi beli.
Bayan ya ji roƙon ko wanne ɓangare, alƙalin ya bada belin wanda a ke ƙara inda zai kawo naira miliyan 2 da kuma wanda zai tsaya masa mutum ɗaya.
Alƙalin ya kuma sanya ranar 21 ga watan Maris domin fara shari’ar.