Kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPC ya bayyana sunan kamfanonin mai na ‘yan kasuwa da yake zargi da shiga da gurɓataccen mai ƙasar, wanda ya haddasa lalacewar ababen hawa.
Shugaban NNPC Mele Kyari ya ce kamfanonin MRS da Oando da Duke Oil da Emadeb ne suka yi dakon man zuwa Najeriya yayin da yake yi wa manema labarai jawabi ranar Laraba.
Ya ce NNPC ya samu rahoton man da ke ɗauke da sinadarin methanol da yawa a cikinsa ranar 20 ga watan Janairun 2022, wanda aka ɗauko daga ƙasar Belgium.
Ya ƙara da cewa duk da ma’aikatansu na hukumar Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority (NMDPRA) sun tantance jiragen da suka yo dakon man kuma suka ba su damar wucewa, aikin tantancewar bai tanadi duba yawan sanadarin methanol ba.
Tun a watan Janairu ne masu ababen hawa suka fara fuskantar dogayen layi a gidajen mai na faɗin ƙasar, abin da NNPC na faruwa sakanakon dakatar da sayar da gurɓataccen man da suka yi.
Shugaban hukumar ta NMDPRA, Faruk Ahmed, ya faɗa wa BBC Hausa yadda aka yi man ya shiga Najeriya da matakin da suka ɗauka.