News
Kwanan nan zan yi rugu-rugu da farashin KeKe NAPEP – Innocent Chukwuma Nwala.
Daga yasir sani abdullahi
Shugaban kamfanin kera motoci na ‘INNOSON’ Chief Innocent Chukwuma Nwala, ya ce nan ba da jimawa ba kamfaninsa zai rugu-rugu da farashin babura masu kafa uku da aka fi sani a wasu jihohin da KEKE NAPEP ko Adaidaita Sahu.
Innocent Chukwuma wanda kamfaninsa ke kera motoci a garin Nnewi dake jihar Anambra, ya ce da zaran sun fara kera baburan na Adaidaita Sahu zai zabtare farashinsu da a kalla kaso hamsin cikin dari kan yadda ake sayarwa a wannan lokaci.
Mista Innocent Chukwuma ya yi wannan alkawari ne a yau alhamis lokacin da shugabannin Cocin Katolika shiyyar jihar suka kai masa ziyara.