Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ƙaddamar da sabbin rukunin gidaje da gwamnatinsa ta gina wa ‘yan gudun hijira a Ƙaramar Hukumar Konduga ranar Laraba.
A cewar gwamnatin jihar, an sake gina gida 803 ne bayan shekara bakwai suna gudun hijira sakamakon hare-haren mayaƙan ƙungiyar Boko Haram.
Wata sanarwa da Isa Gusau, kakakin gwamnatin Borno, ya fitar ta ce Gwamna Zulum ya ba da umarnin a bai wa mutum 500 naira 100,000 kowannensu waɗanda gidajensu ba sa cikin waɗanda aka sake ginawa, inda za a raba musu miliyan 50 jumilla.
Kazalika, gwamnan ya ba da umarnin raba wa maza 240 ‘yan gudun hijirar da suka koma garinsu naira N200,000 kowannensu. Sannan kowace mace daga cikin 379 za ta samu N10,000 da kuma atamfa.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya yaba wa hukumar cigaban yankin arewa maso gabas ta North-East Development Commission (NEDC) bisa taimakon kayan abinci da take ba wa ‘yan gudun hijirar.