Connect with us

News

Firaministan Libya ya sha da ƙyar bayan harin ‘yan bindiga

Published

on

FB IMG 16444820791372649
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Daga yasir sani abdullahi

 

Firaministan Libya Abdulhamid al-Dbeibah ya tsallake rijiya da baya a yunkurin hallaka shi da wasu ‘yan bindiga suka yi.

An yi wa motarsa ɓarin harsasai a lokacin da yake tafiya a birnin Tripoli da safiyar yau Alhamis, amma ba a yi nasarar kama su ba.

Ana ta samun tashin hankali tsakanin kungiyoyin da ba sa jituwa da juna a Libya kan wanda ya dace ya jagoranci kasar.

Nan gaba a yau ne ‘yan majalisa a gabashin ƙasar za su kaɗa ƙuri’ar wanda zai maye gurbin Mista al-Dbeibah, kodayake ya ce ba zai amince da sakamakon kuri’ar ba

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending