Connect with us

News

Rikicin Ukraine: Rasha na shirin fara atasayen soja da Belarus

Published

on

FB IMG 16444820505608561
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

 

 

Rasha ta fara atisayen soja na kwana 10 tare da Belarus ana tsaka da fargabar girke dubban dakarunta a iyakar Ukraine.

Advertisement

Ana sa ran sojojin Rasha 30,000 ne za su shiga atisayen, sai dai mataimakiyar ministan tsaro Ganna Malyar ta ce babu alamun sojojin sun zo da niyyar tayar da husuma.

“Kan halin da ake ciki a bakin iyakarmu, muna iya ganin dandazon sojojin da suka mayar da hankali kan kafa kayan yaki, amma yanzu babu wannan, babu wata alamar barazana,” a cewar ministar.

Belarus babbar ƙawar Rasha ce kuma tana da iyaka mai tsayi da Ukraine ta kudanci.

Advertisement

Amurka ta bayyana atasayen – wanda ake ganin shi ne mafi girma da Rasha za ta yi a Belarus tun bayan yaƙin cacar baka – a matsayin “na tsokana”.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *