News
Yadda cinikin Kiripto yake samun tagomashi a wajen matasa
Daga yasir sani abdullahi
Cinikin Kiripto wanda aka fi sani da ciniki da hada-hadar kuɗin da ake yi ta intanet, tana ƙara samun karɓuwa a tsakankanin matasa.
Harkar Kiripto ɗin dai da wasu suke yi kallon hadarin kaji, tana cigaba da samun tagomashi a wajen matasa, inda har aka fara samun ƙulla yarjejeniya ta musamman a wajen aiwatar da irin wannan ciniki.
Ɗaya daga cikin matasan da suke fafutukar samun ƙwarewa a wannan ciniki, mai suna Imrana Hussain Lucky, ya sanya wata takarda a shafinsa na Fesbuk, inda ya bayyana wata yarjejeniyar ciniki a tsakanin wasu ‘yan kasuwar Kiripto ɗin. Cinikin nasu dai ya doahi kusan naira dubu ɗari huɗu, wanda wasu suke gani a matsayin ganganci.
Ga dai yadda Imaranan ya bayyana a shafinsa game da cinikin. Ya rubuta cewa, “Wannan wata takarda ce da aka yi yarjejeniya a kan sayar da PI.
Allah ya sa wanda ya siya ya siyi alheri wanda ya siyar kuma Allah ya sa kar ya yi nadamar siyarwa.