Babban lauyan gwamnati kuma Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Barrister Musa Abdullahi Lawan,ya bayyana cewa hukumar bayar da tallafin shari’a ta Najeriya (Legal Aid Council of Nigeria) ta nuna aniyarta ta samar da lauyoyin da za su wakilci mutanen da ake zargi da sacewa da kuma kashe yarinyar nan Hanifa Abubakar.
Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa, kwamishinan ya fada mata a ranar Alhamis din nan cewa, matakin ya biyo bayan umarnin da mai shari’a Usman Na’abba na babbar kotun Kano ya yi ne a ranar 5 ga watan nan na Fabrairu cewa gwamnatin jihar ta sama wa babban wanda ake zargin da sauran mutum biyu lauya, kamar yadda suka bukaci lauya ya tsaya musu a shari’ar, saboda ba su da shi.
Babban lauyan na gwamnatin Kano ya ce, a bisa doka duk mutumin da yake fuskantar shari’ar zargin kisan kai, ana bukatar ya samu lauya mai wakiltarsa, idan kuma ba shi da lauyan ba kuma shi da halin dauka, tsarin mulki Najeriya ya sa dole jiha ta sama masa.
Atoni Janar din ya kara bayani da cewa hukumar bayar da tallafin shari’ar ta Najeriya hukuma ce ta tarayya wadda aka kafa ta domin taimaka wa duk wani dan kasar da ba shi da lauya a shari’ar da ake masa mai hukuncin kisa, kyauta.
An dakatar da shari’ar Abdulmalik Tanko da mutum biyu da ake zargi da sacewa da kuma kashe Hanifa saboda ba su da lauyan da zai kare su.
Daman alkalin da ke shari’ar ya dage zama har zuwa ranar 14 ga watan nan na Fabrairu, bayan da ya gabatar da umarnin a sama musu lauya.