News
An kammala shirye-shiryen taron sulhu na ‘APC na gobe-Ganduje
Daga yasir sani Abdullahi
Shugaban kwamitin hadin gwiwa na jam’iyyar APC na kasa/jiha, kuma gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa kwamitin ya kammala shirye-shiryen karbar sauran mambobin kwamitin domin gudanar da taron sasantawa a jihar.
Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, ta ruwaito gwamnan na cewa an tanadi wurin da za a gudanar da taron da aka shirya fara a ranar Juma’a 11 ga watan Fabrairu, 2022 a babban birnin jihar.
Gwamna Ganduje ya tabbatar wa ‘ya’yan sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar cewa a shirye kwamitin ya ke na bayar da tawaga ga duk wanda ya damu da shi da nufin kawo hadin kai da ci gaba a jam’iyyar a jihar da kasa baki daya.
Kwamitin wanda Sakatariyar jam’iyyar ta kasa ta kafa, yana da mambobinsa, Sardaunan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Gwamna Bello Matawalle, Hon. Yakubu Dogara da Sanata Abba Ali.
Kwamitin na da kwanaki bakwai da zai mika rahotonsa.
MALAM MUHAMMAD GARBA
Hon. Kwamishinan yada labarai na jihar Kano
-
News4 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News4 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News4 days ago
DSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

