News
AISHA BUHARI ta yi balaguro a Jirgin Kasa daga KADUNA zuwa ABUJA.

Daga kabiru basiru fulatan
Mai dakin shugaban kasa Hajiya AISHA BUHARI ta koma birnin tarayya Abuja daga KADUNA ta cikin Jirgin Kasa dake zirga-zirga tsakanin biranen biyu.
Rahotanni sun ce uwargidan na shugaban kasa ta bar Kano a cikin Jirgin sama bayan wata ziyarar ta’aziyya da ta kai wa iyalan marigayiya Haneefa Abubakar da na Shehin Malami marigayi Ahmed Bamba, inda daganan KADUNA ta yanke shawarar shiga Jirgin Kasa don komawa birnin tarayya Abuja.
Bayanai sun tabbatar da cewa AISHA BUHARI ta zauna ne cikin Jirgin kusa da kaninta Mahmud Ahmed da sauran ‘yan tawagarta.
Jirgin kasar ya bar KADUNA da misalin karfe hudu dai-dai, inda ya isa birnin tarayya Abuja da misalin karfe shida.
Wannan dai shine karo na farko da mai dakin shugaban kasar ta yi tafiya mai tsayi haka a cikin Jirgin kasa tun bayan da shugaba BUHARI ya hau karagar mulkin kasar nan a shekarar 2015.